Hadisai

Wanda ya yi wanka irin wankan janaba a ranar Juma`a, sannan ya tafi, kamar ya bayar da sadakar rakuma ne

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَنِ اغْتَسَلَ يَوْمَ الجُمُعَةِ غُسْلَ الجَنَابَةِ ثُمَّ رَاحَ، فَكَأَنَّمَا قَرَّبَ بَدَنَةً، وَمَنْ رَاحَ فِي السَّاعَةِ الثَّانِيَةِ، فَكَأَنَّمَا قَرَّبَ بَقَرَةً، وَمَنْ رَاحَ فِي السَّاعَةِ الثَّالِثَةِ، فَكَأَنَّمَا قَرَّبَ كَبْشًا أَقْرَنَ، وَمَنْ رَاحَ فِي السَّاعَةِ الرَّابِعَةِ، فَكَأَنَّمَا قَرَّبَ دَجَاجَةً، وَمَنْ رَاحَ فِي السَّاعَةِ الخَامِسَةِ، فَكَأَنَّمَا قَرَّبَ بَيْضَةً، فَإِذَا خَرَجَ الإِمَامُ حَضَرَتِ المَلاَئِكَةُ يَسْتَمِعُونَ الذِّكْرَ».

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya yi wanka irin wankan janaba a ranar Juma`a, sannan ya tafi, kamar ya bayar da sadakar rakuma ne, wanda ya tafi a lokaci na biyu, kamar ya bayar da sadakar saniya ne. wanda ya tafi a lokaci na uku kamar ya bayar da sadakar rago ne mai ƙaho. wanda ya tafi a lokaci na huɗu kamar ya bayar da kaza ne, wanda kuma ya tafi a lokaci na biyar kamar ya bayar da ƙwai ne. Idan liman ya fito Mala`iku za su halarto suna sauraron zikiri (Huɗuba)".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari game da falalar gaggawar tafiya zuwa sallar Juma'a. Gaggawa tana farawa ne daga bullowar rana zuwa lokacin zuwan liman; shi ne sa'o'i biyar, ana karkasasu kaso biyar gwargwadan lokaci tsakanin bullowar rana har zuwa shigowar liman da hawansa minbari dan huɗuba: Na farko: Wanda ya yi wanka cikakke kamar wankan janaba, sannan ya tafi masallacin Juma'a a lokaci na farko kamar ya yi sadaka da taguwa ne. Na biyu: Wanda ya tafi a lokaci na biyu kamar ya yi sadaka da saniya ne. Na uku; Wanda ya tafi a lokaci na uku kamar ya yi sadaka ne da rago - shi ne namijin tinkiya - mai ƙahuhhuna. Na huɗu: Wanda ya tafi a lokaci na huɗu kamar ya yi sadaka ne da kaza. Na biyar: Wanda ya tafi a lokaci na biyar kamar ya yi sadaka ne da ƙwai. Idan liman ya fito dan huɗuba; sai mala'ikun da suke zaune a ƙofofi dan rubuta masu shiga masallaci na farko da mai biye da shi sai su dakatar da rubutu, sai su zo suna jin zikiri da huɗuba.

Fa'idoji

  • Kwaɗaitarwa akan yin wanka ranar Juma'a, kuma yana kasancewa ne kafin tafiya zuwa sallah.
  • Falalar gaggawa zuwa sallar Juma'a daga farkon sa'o'in yini.
  • Kwaɗaitarwa akan gaggawa ga ayyuka na gari.
  • Halartowar mala'iku sallar Juma'a da sauraransu ga huɗuba.
  • Mala'iku suna ƙofofin masallatai, suna rubuta masu shigowa, na farko sai mai beye da shi, a zuwa sallar Juma'a.
  • Ibnu Rajab ya ce: Faɗinsa: "Wanda ya yi wanka ranar Juma'a, sannan ya tafi" yana nuni akan cewa wankan da ake so dan Juma'a farkonsa shi ne bullowar alfijir, ƙarshensa kuma tafiya zuwa Juma'a.
Sharhi: العربية

يُخبِرُ النبيُّ صلى الله عليه وسلم عن فَضْل التَّبْكِيْر في الذهاب إلى صلاة الجمعة، ويبدأ التبكير من طلوع الشمس إلى مجيء الإمام؛ وهو خمس ساعات، وتقسم على حسب الوقت بين طلوع الشمس إلى دخول الإمام وصعوده المنبر للخطبة خمسة أجزاء: الأول: من اغتسل غسلًا كاملًا كغسل الجنابة، ثم ذهب لمسجد الجمعة في الساعة الأولى فكأنما تصدَّق بِجَمَل. الثاني: من ذهب في الساعة الثانية فكأنما تصدَّق ببقرة. الثالث: من ذهب في الساعة الثالثة فكأنما تصدق بكبش -وهو ذكر الضأن- له قرون. الرابع: من ذهب في الساعة الرابعة فكأنما تصدق بدجاجة. الخامس: من ذهب في الساعة الخامسة فكأنما تصدق ببيضة. فإذا خرج الإمام للخطبة؛ توقَّفت الملائكة الجالسون على الأبواب لكتابة الداخلين للمسجد الأول فالأول عن الكتابة، وجاؤوا يستمعون الذكر والخطبة.

  • الحث على الاغتسال يوم الجمعة، ويكون قبل الذهاب إلى الصلاة.
  • فضيلة التبكير إلى صلاة الجمعة من أول ساعات النهار.
  • الحث على المبادرة إلى الأعمال الصالحة.
  • حضور الملائكة صلاة الجمعة واستماعهم للخطبة.
  • الملائكة على أبواب المساجد، يكتبون القادمين، الأوّل فالأول، في المجيء إلى صلاة الجمعة.
  • قال ابن رجب: قوله: "من اغتسل يوم الجمعة، ثم راح" يَدُلّ على أن الغُسل المستحب للجمعة أوّله طلوع الفجر، وآخره الرواح إلى الجمعة.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari