Hadisai

Lallai cewa kwatankwacin ma’abocin Alƙur'ani kamar kwatankwacin ma'abocin dabaibayayyun raƙuma ne, idan ya kula da su sai ya riƙesu, idan kuma ya sakesu sai su tafi

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنِ ابْنِ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِنَّمَا مَثَلُ صَاحِبِ القُرْآنِ كَمَثَلِ صَاحِبِ الإِبِلِ المُعَقَّلَةِ، إِنْ عَاهَدَ عَلَيْهَا أَمْسَكَهَا، وَإِنْ أَطْلَقَهَا ذَهَبَتْ».

Fassara

Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai cewa kwatankwacin ma’abocin Alƙur'ani kamar kwatankwacin ma'abocin dabaibayayyun raƙuma ne, idan ya kula da su sai ya riƙesu, idan kuma ya sakesu sai su tafi".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kamanta wanda ya karanta Alƙur'ani kuma ya saba da karanta shi - daidai ne yana dubawa daga Mushafi ne ko da ka yake yi - da ma'abocin dabaibayayyun raƙuma da igiyar da ake ɗaure gwiwowin raƙuma da su, idan ya kula sai ya ci gaba da riƙesu, idan kuma ya saki ɗaurinsu sai su tafi su suɓuce, idan ma'abocin Alƙur'ani ya tsaya sai ya karanta shi zai tuna shi, idan kuma bai tsayu da shi ba to zai manta shi; lazimta ba zata gushe tana samammiya ba sai hadda itama ta zama tana nan.

Fa'idoji

  • Kwaɗaitarwa akan lazimtara Alƙur'ani da kuma karanta shi, da kiyayewa daga bijirar da shi ga mantuwa.
  • Dawwama akan karatun Alƙur'ani harshensa zai horu da shi kuma karanta shi zai yi masa sauƙi, idan ya ƙaurace masa sai karatun ya yi masa nauyi kuma ya wahalar da shi.
  • Alƙali ya ce: Ma'anar "Ma'abocin Alƙur'ani" wato: Wanda ya saba da shi, al-Musahaba: Sabo da abu, daga haka ne: Wane abokin wane ne, da 'yan aljanna da kuma 'yan wuta.
  • Daga cikin hanyoyin Da'awah akwai buga misalai.
  • Ibnu Hajar ya ce: An keɓanci raƙuma da ambato; domin cewa sune mafi tsananin gujewa cikin dabbobin gida, kuma kama su bayan sun gudu akwai wahala.
Sharhi: العربية

شَبَّهَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم من دَرَس القرآن وأَلِفَ تلاوته -سواء نظرًا من المصحف أو عن ظهر قلب- بصاحب الإبل المعقلة بالحبل الذي يُشَدُّ به رُكْبة البعير، إن عاهد عليها استمر إمساكه لها، وإن أطلق عُقُلَها ذهبت وانفلتت، فإذا قام صاحب القرآن فقرأه ذَكَره، وإذا لم يقم به نسيه؛ فما زال التعاهد موجودًا فالحفظ موجود.

  • الحث على تعاهد القرآن وتلاوته، والحذر من تعريضه للنسيان.
  • المداومة على قراءة القرآن يذلُّ له لسانه ويسهل عليه قراءته، فإذا هَجَره ثقلت عليه القراءة وشقّت عليه.
  • قال القاضي: ومعنى "صاحب القرآن" أي: الذي ألِفه، والمصاحبة: المُؤالَفة، ومنه: فلان صاحب فلان، وأصحاب الجنة وأصحاب النار.
  • من أساليب الدعوة ضرب الأمثال.
  • قال ابن حجر: وخص الإبل بالذكر؛ لأنها أشد الحيوان الإنسي نفورًا، وفي تحصيلها بعد استمكان نفورها صعوبة.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari