Hadisai

Wanda ya rantse sai ya ce a cikin rantsuwarsa: Na rantse da Lata da Uzza, to ya ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, wanda ya ce wa abokinsa: Zo mu yi caca tare, to ya yi sadaka

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ حَلَفَ فَقَالَ فِي حَلِفِهِ: وَاللَّاتِ وَالعُزَّى، فَلْيَقُلْ: لاَ إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، وَمَنْ قَالَ لِصَاحِبِهِ: تَعَالَ أُقَامِرْكَ، فَلْيَتَصَدَّقْ».

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya rantse sai ya ce a cikin rantsuwarsa: Na rantse da Lata da Uzza, to ya ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, wanda ya ce wa abokinsa: Zo mu yi caca tare, to ya yi sadaka".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana gargaɗi akan rantsuwa da wanin Allah; inda mumini ba ya rantsuwa sai da Allah kadai, kuma yana bada labarin cewa wanda ya yi rantsuwa da wanin Allah; kamar wanda ya yi rantsuwa ga misali da: Lata da Uzza - su biyun gumaka ne da ake bauta musu a lokacin Jahiliyya kafin Musulunci - to ya wajaba akansa ya ce yana mai riskar abin da ya fada da kansa: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, dan kuɓuta daga shirka, da kaffara daga wannan rantsuwar tasa. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bada labarin cewa wanda ya ce wa abokinsa: Zo mu yi wasan caca, - ita ce mutum ko sama da haka su yi rinjayeyeniya akan wata dukiyar da wani zai ɗauka a tsakaninsu, kuma kowanne daya daga cikinsu ba ya zama haka kodai yaci riba a cikinta ko kuma ya faɗi -; to an so ya yi sadaka da wani abu dan kaffara daga abinda ya yi kira zuwa gare shi.

Fa'idoji

  • Rantsuwa bata kasancewa sai da Allah da sunayenSa da kuma siffofinSa.
  • Rantsuwa da wanin Allah - Maɗaukakin sarki - haramun ce, daidai ne rantsuwace da gumaka kamar Lata da Uzza, ko rantsuwa da amana, ko rantsuwa da Annabi ko wanin hakan.
  • AlKhaɗɗabi ya ce: Rantsuwa kawai tana kasancewa ne da abin da ake bautawa abin girmamawa, idan ya yi rantsuwa da Lata da makacinsa to haƙiƙa ya yi kama da kafirai, sai aka umarce shi ya riski abinda ya fada da kalmar Tauhidi.
  • Babu kaffarar rantsuwa akan wanda ya yi rantsuwa da wanin Allah, kawai ya wajaba akan shi ya koma ga Allah da neman gafara; domin ta wuce ayi mata kaffara sai dai tuba.
  • Haramcin caca da dukkan surorinta da yanayinta, itace cacar da Allah - Maɗaukakin sarki - Ya haramta kuma Ya haɗata da giya da gumaka.
  • Wajabcin barin saɓo a lokacin aikata shi .
  • Wanda ya afka a cikin wani mummunan abu to ya wajaba akansa ya bi shi da kyakkyawa; domin kyawawan ayyuka suna tafiyar da munanan ayyuka.
Sharhi: العربية

يُحَذِّرُ النبيُّ صلى الله عليه وسلم مِن الحَلِف بغير الله؛ حيث المؤمن لا يحلف إلا بالله، ويخبر أنّ من حلف بغير الله؛ كمن حلف مثلًا: باللات والعُزى -وهما صنمان كانا يُعبدان في الجاهلية قبل الإسلام- فيجب عليه أن يقول مستدركًا على نفسه: لا إله إلا الله، تبرؤًا من الشرك، وكفارةً عن حلفه ذاك. ثم أخبر صلى الله عليه وسلم أنّ من قال لصاحبه: تعال نلعب القمار، -وهو أن يتغالب اثنان فأكثر على أن يكون بينهم مال يأخذه الغالب، ولا يخلو كل واحد منهما فيه من أن يغنم أو يغرم-؛ فيستحب أن يتصدق بشيء تكفيرًا عما دعا إليه.

  • الحلف لا يكون إلا بالله وأسمائه وصفاته.
  • الحلف بغير الله تعالى محرَّم، سواء الحلف بالأصنام كاللات والعزى، أو الحلف بالأمانة، أو الحلف بالنبي أو غير ذلك.
  • قال الخطابي: اليمين إنما تكون بالمعبود المعظّم، فإذا حلف باللات ونحوها فقد ضاهى الكفار، فأمر أن يتدارك بكلمة التوحيد.
  • ليس على من حلف بغير الله كفارة يمين، وإنما يلزمه الإنابة والاستغفار؛ لأنه أعظم من أن تكفِّرَه غير التوبة.
  • تحريم القمار بكل صوره وأشكاله، وهو الميسِر الذي حرَّمه الله تعالى وقرَنه بالخمر والأصنام.
  • وجوب الرجوع عن المعصية في حال اقترافها.
  • من وقع في سيئة عليه أن يتبعها حسنة؛ لأن الحسنات يذهبن السيئات.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari