Hadisai

Wanda ya ga wani mummunan abu daga cikinku, to ya canza shi da hannunsa, idan ba zai iya ba to (ya canza shi) da harshe, idan ba zai iya ba to (ya canza shi) da zuciyarsa, wannan shi ne mafi raunin imani

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عن أبي سعيد الخُدْريِّ رضي الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «‌مَنْ ‌رَأَى ‌مِنْكُمْ ‌مُنْكَرًا فَلْيُغَيِّرْهُ بِيَدِهِ، فَإِنْ لَمْ يَسْتَطِعْ فَبِلِسَانِهِ، فَإِنْ لَمْ يَسْتَطِعْ فَبِقَلْبِهِ، وَذَلِكَ أَضْعَفُ الْإِيمَانِ».

Fassara

Daga Abu Sa'id Al-Kudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- yana cewa: "Wanda ya ga wani mummunan abu daga cikinku, to ya canza shi da hannunsa, idan ba zai iya ba to (ya canza shi) da harshe, idan ba zai iya ba to (ya canza shi) da zuciyarsa, wannan shi ne mafi raunin imani".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana yin umarni da canza abin ki - wanda shi ne dukkanin abinda Allah da ManzonSa suka hana - gwargwadon iko, Idan ya ga wani abin ki to yana wajaba akansa ya canja shi da hannu idan yana da iko, Idan ya gajiya akan hakan, to ya canja shi da harshensa, ta hanyar hana mai aikatawar, kuma ya bayyana masa cutar hakan, ya kuma shiryar da shi zuwa alheri maimakon wannan sharrin, Idan ya gajiya daga wannan matakin, to ya canja shi da zuciyarsa shi ne ya ki wannan mummunan aikin, kuma ya yi niyyar cewa shi da yana da iko akan canja shi to da ya aikata, canzawa da zuciya shi ne mafi raunin matakan imani a canja abin ki.

Fa'idoji

  • Hadisn asali ne a bayanin matakan canza abin ki.
  • Umarni da bi sannu-sannu a hani ga abin ki, kowa gwargwadon iyawarsa da ikonsa.
  • Hani daga abin ki wani babi ne mai girma a Addini kuma ba ya faduwa akan wani mutum, kuma ana dorawa kowanne musulmi shi gwargwadon ikonsa.
  • Umarni da aikin alheri da hani daga abin ki yana daga dabi'un imani, kuma imani yana karuwa yana kuma raguwa.
  • Ana sharadantawa a hani daga abin ki: Sanin cewa wannan aikin abin ki ne.
  • Ana shardantawa a canja abin ki: Cewa kada wani abin kin mafi girma daga gare shi ya biyo baya.
  • Akwai wasu ladubba da sharuddan da yake kamata ga musulmi ya sansu ga hani daga abin ki.
  • Hani daga abin ki yana bukatuwa zuwa ga siyasa ta shari'a, kuma da ilimi da basira.
  • Rashin inkari da zuciya yana nuni ga raunin imani.
Sharhi: العربية

يأمر النبي صلى الله عليه وسلم بتغيير المنكر -وهو كل ما نهى الله عنه ورسوله- حسب الاستطاعة، فإذا رأى منكرًا فيجب عليه تغييره باليد إن كان له قدرة، فإن عجز عن ذلك فليغيره بلسانه بأن ينهى مرتكبه ويُبيِّن له ضرره ويرشده إلى الخير بدل هذا الشر، فإن عجز عن هذه المرتبة فليغيره بقلبه بأن يَكرَه هذا المنكر ويَعزِم أنه لو قدر على تغييره لفعل، والتغيير بالقلب أضعف مراتب الإيمان في تغيير المنكر.

  • الحديث أصل في بيان مراتب تغيير المنكر.
  • الأمر بالتَّدَرُّج في النهي عن المنكر، كلٌّ بحسب استطاعته وقدراته.
  • النهي عن المنكر باب عظيم في الدين ولا يسقط عن أحد، ويُكَلَّف به كل مسلم بحسب استطاعته.
  • الأمر بالمعروف والنهي عن المنكر من خصال الإيمان، والإيمان يزيد وينقص.
  • يشترط في النهي عن المنكر: العلم بكون ذلك الفعل منكرًا.
  • يشترط في تغيير المنكر: أن لا يترتب عليه منكر أعظم منه.
  • للنهي عن المنكر آداب وشروط ينبغي على المسلم أن يتعلمها.
  • إنكار المنكر يحتاج إلى سياسة شرعية، وإلى علم وبصيرة.
  • عدم الإنكار بالقلب يدل على ضعف الإيمان.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari