Hadisai

Lalle cewa hakkin Allah akan bayi su bauta maSa kada su hada shi komai, hakkin bayi ga Allah ba zai azabtar da wanda bai tarayya daShi da komaiba

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ مُعَاذٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: كُنْتُ رِدْفَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَلَى حِمَارٍ يُقَالُ لَهُ عُفَيْرٌ، فَقَالَ: «يَا مُعَاذُ، هَلْ تَدْرِي حَقَّ اللَّهِ عَلَى عِبَادِهِ، وَمَا حَقُّ العِبَادِ عَلَى اللَّهِ؟»، قُلْتُ: اللَّهُ وَرَسُولُهُ أَعْلَمُ، قَالَ: «فَإِنَّ حَقَّ اللَّهِ عَلَى العِبَادِ أَنْ يَعْبُدُوهُ وَلا يُشْرِكُوا بِهِ شَيْئًا، وَحَقَّ العِبَادِ عَلَى اللَّهِ أَنْ لا يُعَذِّبَ مَنْ لا يُشْرِكُ بِهِ شَيْئًا»، فَقُلْتُ: يَا رَسُولَ اللَّهِ أَفَلاَ أُبَشِّرُ بِهِ النَّاسَ؟ قَالَ: «لا تُبَشِّرْهُمْ، فَيَتَّكِلُوا».

Fassara

Daga Mu'az - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance a bayan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan wani jaki ana ce masa Ufair, sai ya ce: "Ya Mu'az, shin kasan hakkin Allah akan bayin Sa, kuma menene hakkin bayi ga Allah?", sai na ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani, ya ce: "Lalle cewa hakkin Allah akan bayi su bauta maSa kada su hada shi komai, hakkin bayi ga Allah ba zai azabtar da wanda bai tarayya daShi da komaiba", sai na ce: Ya Manzon Allah shin ba nayiwa mutane albishir da shi ba? Ya ce: "Kada ka yi musu albishir, sai su dogara".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana hakkin Allah akan bayi, da hakkin bayi ga Allah, lallai cewa hakkin Allah akan bayi su bauta maSa Shi kadai kada su hada shi da wani abu. Kuma cewa hakkin bayi ga Allah shi ne ba zai azabtar da masu kadaitaShi da bauta ba, wadanda ba sa sanya masa abokin tarayya ba. Sannan cewa Mu'az, ya ce: Ya Manzon Allah, shin baa a yi wa mutane albishir da shi ba dan su yi farinciki, kuma su yi murna da wannan falalar ba ?? Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana shi dan tsoron kada su dogara akanta.

Fa'idoji

  • Bayanin hakkin Allah - madaukakin sarki - wanda ya wajabta shi akan bayinSa, shi ne su bauta maSa, kada su hada da komai.
  • Bayanin hakkin bayi ga Allah - madaukakin sarki - wanda Ya wajabtaShi akan kanSa dan falala daga gareShi da kuma ni'ima, shi ne Ya shigar da su Aljanna, kada ya azabtar da su.
  • A cikinsa akwai albishir mai girma ga masu kadaita Allah wadanda ba sa taranya wani abu daShi da cewa makomarsu (ita ce) shiga Aljanna.
  • Mu'azu ya karantar da wannan Hadisin kafin mutuwarsa; dan tsoron fadawa a cikin zunubin boye ilimi.
  • Fadakarwa akan rashin yada sashin Hadisai ga wasu mutane dan tsoron kada wanda bai riski ma'anarsuba; wannan a cikin abinda a karkashinsa babu wani aiki, kuma babu wani haddi daga haddodin Shari’a..
  • Masu kadaita Allah masu sabo suna karkashin ganin damar Allah, in Yaso ya yi musu azaba, idan kuma Yaso Ya gafarta musu, sannan makomarsu tana ga Aljanna.
Sharhi: العربية

يبين النبي صلى الله عليه وسلم حق الله على العباد، وحق العباد على الله، وأن حق الله على العباد أن يعبدوه وحده ولا يشركوا به شيئًا، وأن حق العباد على الله هو أن لا يُعذب الموحدين الذين لا يشركون به شيئًا. ثم إن معاذا قال: يا رسول الله، ألا أبشر الناس ليفرحوا ويستبشروا بهذا الفضل؟ فنهاه النبي صلى الله عليه وسلم خشية أن يعتمدوا عليها.

  • بيان حقّ الله تعالى الذي أوجبه على عباده، وهو أن يعبدوه، ولا يشركوا به شيئًا.
  • بيان حقّ العباد على الله تعالى الذي أوجبه على نفسه فضلًا منه ونعمةً، وهو أن يدخلهم الجَنَّة، ولا يعذبهم.
  • فيه بشارة عظيمة للموحّدين الذين لا يشركون بالله تعالى شيئاً بأن مصيرهم دخول الجَنَّة.
  • حَدَّثَ معاذ بهذا الحديث قبل موته؛ مخافة الوقوع في إثم كتمان العلم.
  • التنبيه على عدم نشر بعض الأحاديث عند بعض الناس خوفًا على من لم يدرك معناها؛ وذلك فيما ليس تحته عمل ولا فيه حد من حدود الشريعة.
  • عصاة الموحدين تحت مشيئة الله إن شاء عذّبهم وإن شاء غفر لهم، ثم مصيرهم إلى الجنة.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari