Hadisai

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci wani abu, sai ya ce: "Wannan a lokacin tafiyar ilimi kenan

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce ne ta wani bangarenIbnu Majah ne ya ruwaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ زِيَادِ بْنِ لَبِيدٍ رضي الله عنه قَالَ: ذَكَرَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ شَيْئًا، فَقَالَ: «ذَاكَ عِنْدَ أَوَانِ ذَهَابِ الْعِلْمِ» قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، وَكَيْفَ يَذْهَبُ الْعِلْمُ، وَنَحْنُ نَقْرَأُ الْقُرْآنَ وَنُقْرِئُهُ أَبْنَاءَنَا وَيُقْرِئُهُ أَبْنَاؤُنَا أَبْنَاءَهُمْ إِلَى يَوْمِ الْقِيَامَةِ؟ قَالَ: «ثَكِلَتْكَ أُمُّكَ زِيَادُ، إِنْ كُنْتُ لَأُرَاكَ مِنْ أَفْقَهِ رَجُلٍ بِالْمَدِينَةِ، أَوَلَيْسَ هَذِهِ الْيَهُودُ وَالنَّصَارَى يَقْرَؤونَ التَّوْرَاةَ وَالْإِنْجِيلَ، لَا يَعْمَلُونَ بِشَيْءٍ مِمَّا فِيهِمَا؟!».

Fassara

Daga Ziyad Dan Labid - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci wani abu, sai ya ce: "Wannan a lokacin tafiyar ilimi kenan" Na ce: Ya Manzon Allah, ta yaya ilimi zai tafi, alhali mu muna karanta Alkur’ani kuma, muna karantar da 'ya'yanmu shi, kuma 'ya'yanmu suna karantar da 'ya'yansu har zuwa ranar Alkiyama ? Ya ce: "Mahaifiyarka ta yi wabinka Ziyad, na kasance ina ganinka daga mafi fahimtar mutane a Madina, shin wadannan Yahudawan da Nasaran ba sa karanta Attaura da Injila, ba sa aiki da wani abinda ke cikinsu?!".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agar shi - ya kasance a zaune tsakanin sahabbansa, sai ya ce:: Wannan lokacin da za'a dauke a zare ilimi ne daga mutane. Sai Ziyad Dan Labid Al-Ansary - Allah Ya yarda da shi - ya yi mamaki kuma ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, Sai ya ce; Ta yaya za'a dauke ilimi a sarayar da shi daga garemu?! Alhali mun karanta Alkur’ani mun haddaceshi; na rantse da Allah sai mun karantashi, kuma mun karantar da matanmu da 'ya'yanmu shi, da 'ya'yan 'ya'yanmu, Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce yana mai mamaki: Mahaifiyarka ta rasaka ya Ziyad! na kasance ina lissafaka daga malaman mutanen Madina! Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bayyana masa: Cewa rasa ilimi bai zamo da rasa Alkur’ani ba; saidai rasa ilimi (yana kasancewa ne) da rashin aiki da shi, Wannan Attaurar da Injilar dake wajen Yahudawa da Nasara; a tare da haka ba ta anfanesu ba, kuma ba su anfana da manufarsu ba; shi ne aiki da abinda suka sani.

Fa'idoji

  • Samun kwafin Alkur’ani da littattafai a hannun mutane ba ya anfani ba tare da aiki da su ba.
  • Dauke ilimi yana kasancewa da wasu al'amura, daga cikin su (akwai): Mutuwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, da mutuwar malamai, da barin aiki da ilimi.
  • Daga alamomin Alkiyama (akwai) tafiyar ilimi da barin aiki da shi.
  • Kwadaitarwa akan aiki da ilimi domin shi ne abin nufi.
Sharhi: العربية

كان النبي صلى الله عليه وسلم جالسًا بين أصحابه، فقال: هذا الوقت الذي يُرفَع ويُسلَب فيه العلم من الناس، فتعجب زياد بن لبيد الأنصاري رضي الله عنه وسأل النبي صلى الله عليه وسلم، فقال: كيف يرفع العلم ويضيع منا؟! وقد قرأنا القرآن وحفظناه؛ فوالله لنَقرأنَّه، ولنُقرِئنَّه نساءنا وأبناءنا، وأبناء أبنائنا، فقال النبي صلى الله عليه وسلم متعجبًا: فقدتْك أمك يا زياد! إن كنت لأعدك من علماء أهل المدينة! ثم بين له صلى الله عليه وسلم: أنَّ فقد العلم ليس بفقد القرآن؛ ولكن فقد العلم بفقد العمل به، فهذه التوراة والإنجيل عند اليهود والنصارى؛ ومع ذلك ما نفعتهم، وما استفادوا من مقصودهما؛ وهو العمل بما علموا.

  • وجود المصاحف والكتب بأيدي النّاس لا تنفع بدون العمل بها.
  • رفع العلم يكون بأمور، منها: موت النبي صلى الله عليه وسلم، وموت العلماء، وترك العمل بالعلم.
  • من علامات الساعة ذهاب العلم وترك العمل به.
  • الحث على العمل بالعلم فإنه هو المقصود.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari