Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضيَ اللهُ عنهُ أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «لَوْ يَعْلَمُ النَّاسُ مَا فِي النِّدَاءِ وَالصَّفِّ الْأَوَّلِ ثُمَّ لَمْ يَجِدُوا إِلَّا أَنْ يَسْتَهِمُوا عَلَيْهِ لَاسْتَهَمُوا، وَلَوْ يَعْلَمُونَ مَا فِي التَّهْجِيرِ لَاسْتَبَقُوا إِلَيْهِ، وَلَوْ يَعْلَمُونَ مَا فِي الْعَتَمَةِ وَالصُّبْحِ لَأَتَوْهُمَا وَلَوْ حَبْوًا».
Fassara
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Da a ce mutane suna sanin abinda ke cikin kiran sallah (na lada) da kuma sahu na farko sannan ba za su samu ba sai idan sun yi ƙuri'a a kansa da sun yi ƙuri'a, kuma da a ce suna sanin abinda ke cikin gaggawa (zuwa sallah a farkon lokaci) da sun yi gasar zuwa gare shi, kuma da a ce suna sanin abinda ke cikin sallar dare (Issha) da Asuba da sun zo musu koda da jan ciki ne».
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mutane da a ce suna sanin abinda ke cikin kiran sallah da sahun farko na falala da alheri da albarka sannan ba za su samu damar samun shi ba sai sun yi ƙuri'a akan sa, waye a cikinsu ya fi cancanta akan ɗan uwansa ? da sun yi ƙuri'a, kuma da a ce suna sanin abinda ke cikin gaggawa zuwa sallah a farkon lokacinta da sun yi rigegeniya gareta, kuma da a ce suna sanin gwargwadan lada a zuwa sallar Issha'i da sallar Asuba da zuwa gare su ya yi sauƙi koda da jan ciki ne akan gwiwowi kamar yadda yaro yake tafiya a farkon al'amarinsa.
Fa'idoji
- Bayanin falalar kiran sallah.
- Bayanin falalar sahun farko, da kuma kusanci ga liman.
- Bayanin falalar gaggawa zuwa sallah a farkon lokacinta da akafi so; dan abinda ke cikinsa na falala mai girma, da kuma abinda ke biye da shi na fa'idoji, daga cikinsu akwai: Riskar sahun farko, da riskar sallah a farkon lokacinta, da yin nafila, da karatun AlƘur'ani, da samun istigfarin mala'iku gare shi, kuma cewa shi ba zai gushe ba acikin sallah muddin dai ya jiran sallah, da wanin hakan.
- Kwaɗaitarwa mai girma akan halartar jam’i na waɗannan sallolin biyu, da falala mai yawa a cikin hakan dan abinda ke cikinsu na wahala akan rai na gurɓata farkon baccinta da kuma ƙarshensa, saboda haka ne suka zama mafi nauyin sallah akan munafukai.
- Nawawi ya ce: A cikinsa akwai tabbatar da ƙuri'a a cikin haƙƙoƙin da mutane suke cunkoso a kansu kuma suke jayya a cikinsu.
- Sahun farko ya fi na uku, na uku yafi na huɗu, da dai sauransu.
Sharhi: العربية
أخبر النبيُّ صلى الله عليه وسلم أن الناس لو يعلمون ما في الأذان والصف الأول من الفضيلة والخير والبركة ثم لم يجدوا من وجوه التقديم والأولوية لها إلا أن يقترعوا عليهما أيهم يستحق على صاحبه لاقترعوا، ولو يعلمون ما في التبكير إلى الصلاة في أول وقتها لاستبقوا إليه، ولو يعلمون مقدار الثواب في إتيان صلاة العشاء وصلاة الفجر لاستسهل إتيانهما ولو حبوًا على الرُّكَب كما يمشي الصبي أول أمْرِه.
- بيان فضيلة الأذان.
- بيان فضيلة الصف الأول، والقُرْب من الإمام.
- بيان فضيلة التبكير إلى الصلاة في أول وقتها المستحب؛ لِما فيه من الفضل العظيم، وما يترتب عليه من الفوائد، ومنها: إدراك الصف الأول، وإدراك الصلاة من أولها، وأداء النافلة، وقراءة القرآن، وحصول استغفار الملائكة له، وأنه لا يزال في صلاة ما انتظر الصلاة، وغير ذلك.
- الحث العظيم على حضور جماعة هاتين الصلاتين، والفضل الكثير في ذلك لما فيهما من المشقة على النفس من تَنْغِيْص أول نومها وآخره، ولهذا كانتا أثقل الصلاة على المنافقين.
- قال النووي: فيه إثبات القرعة في الحقوق التي يزدحم عليها ويتنازع فيها.
- الصف الثاني أفضل من الثالث، والثالث أفضل من الرابع، وهلم جرًّا.