Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ عَبْدِ اللهِ بنِ مَسْعُودٍ رَضيَ اللهُ عنهُ قَالَ: نَامَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَلَى حَصِيرٍ، فَقَامَ وَقَدْ أَثَّرَ فِي جَنْبِهِ، فَقُلْنَا: يَا رَسُولَ اللهِ، لَوِ اتَّخَذْنَا لَكَ وِطَاءً، فَقَالَ: «مَا لِي وَلِلدُّنْيَا، مَا أَنَا فِي الدُّنْيَا إِلاَّ كَرَاكِبٍ اسْتَظَلَّ تَحْتَ شَجَرَةٍ ثُمَّ رَاحَ وَتَرَكَهَا».
Fassara
Daga Abdullahi ɗan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi bacci akan wata tabarma, sai ya tashi haƙiƙa ta yi masa tabo a gefensa, sai muka ce: Ya manzon Allah, inama dai a ce mun yi shimfiɗa saboda kai, sai ya ce: "Matsayina da duniya, ni a cikinta ba komai bane sai kamar matafiyi ne akan abin hawa da ya sha inuwa a ƙarƙashin wata bishiya sannan ya tafi ya barta".
Sharhi
Abdullahi ɗan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ambaci cewa annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi bacci akan shimfiɗa ƙarama wacce aka saƙata da wasu daga tsirrai, sai ya miƙe alhali tabarmar ta yi tabo a fatar gefensa, sai muka ce: Ya manzon Allah, ina ma dai a ce mu yi maka wata shimfiɗa mai laushi da hakan ya fi kyau daga kwanciyarka akan wannan tabarmar mai kaushi, sai (annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ni bana son sabo da duniya har in yi kwaɗayi a cikinta, kwatankwacina da wanzuwa a cikin duniya bai zama ba sai kamar wani matafiyi ne da ya sha inuwa ƙarƙashin wata bishiya sannan ya tafi ya barta.
Fa'idoji
- Bayanin abinda annabi - tsira da amincin Allah su tabbat agare shi - yake akansa na gudun duniya da bijire mata.
- A cikin Hadisin babu barin abinda babu makawa gare shi na duniya, kawai shagalta da ita ne akan lahira, domin mutum ya sha inuwar bishiya kuma ya fa'idantu da ita saboda isarsa, bai kuma karkata zuwa gareta ba.
- Yin izina da halin annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, domin cewa shi ne koyi mai kyau, kuma cewa wanda ya bi sawunsa to ya shiriya, kuma ya rabauta a duniya da lahira.
- Kwaɗayin sahabbai - Allah Ya yarda da su - akan manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbat agare shi - da kuma soyayyarsu gare shi.
- Halaccin buga misalai a cikin Da'awah da kuma koyarwa.
Sharhi: العربية
ذكر عبد الله بن مسعود رضي الله عنه أن النبي صلى الله عليه وسلم نام على بِساط صغير مَنْسُوْج من بعض النبات، فقام وقد أثّر الحصير في جلد جنبه، فقلنا: يا رسول الله، لو اتخذنا لك فراشًا ليّنًا لكان أحسن من اضطجاعك على هذا الحصير الخشن، فقال صلى الله عليه وسلم: ليس لي محبة وأُلْفة مع الدنيا حتى أرغب إليها، فما مثلي والبقاء في الدنيا إلا كراكب استظل تحت شجرة ثم راح وتركها.
- بيان ما كان عليه النبي صلى الله عليه وسلم من الزهد في الدنيا والإعراض عنها.
- ليس في الحديث ترك ما لا بد منه من الدنيا، وإنما الانشغال بها عن الآخرة، فإن الرجل استظل بالشجرة واستفاد منها من أجل وصوله، ولم يركن إليها.
- الاعتبار بحال النبي صلى الله عليه وسلم، فإنه الأسوة الحسنة، وأن من اقتفى آثاره اهتدى، وأفلح في الدنيا والآخرة.
- حرص الصحابة رضي الله عنهم على رسول الله صلى الله عليه وسلم ومحبتهم له.
- مشروعية ضرب الأمثال في الدعوة والتعليم.