Hadisai

Wanda ya gangaro daga wani dutse sai ya kashe kansa to shi yana cikin wuta zai dinga gangarowa a cikinta yana abin dawwamarwa a cikinta har abada

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَنْ تَرَدَّى مِنْ جَبَلٍ فَقَتَلَ نَفْسَهُ فَهُوَ فِي نَارِ جَهَنَّمَ يَتَرَدَّى فِيهِ خَالِدًا مُخَلَّدًا فِيهَا أَبَدًا، وَمَنْ تَحَسَّى سُمًّا فَقَتَلَ نَفْسَهُ فَسُمُّهُ فِي يَدِهِ يَتَحَسَّاهُ فِي نَارِ جَهَنَّمَ خَالِدًا مُخَلَّدًا فِيهَا أَبَدًا، وَمَنْ قَتَلَ نَفْسَهُ بِحَدِيدَةٍ فَحَدِيدَتُهُ فِي يَدِهِ يَجَأُ بِهَا فِي بَطْنِهِ فِي نَارِ جَهَنَّمَ خَالِدًا مُخَلَّدًا فِيهَا أَبَدًا».

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Wanda ya gangaro daga wani dutse sai ya kashe kansa to shi yana cikin wuta zai dinga gangarowa a cikinta yana abin dawwamarwa a cikinta har abada, wanda ya tsotsi wata gubar sai ya kashe kansa to gubarsa tana hannunsa zai dinga tsotsarta a cikin wutar Jahannama yana madawwami a cikinta har abada, wanda ya kashe kansa da wani ƙarfe to ƙarfen zai zama a hannunsa zai dinga cakawa cikinsa shi a cikin wutar Jahannama yana madawwami har abada a cikinta».

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa wanda ya yi gangancin kashe kansa gargaɗi a duniya cewa za’a yi masa uƙuba a ranar alƙiyama a cikin wutar Jahannama ta irin hanyar da ya yi wa kansa a duniya dan sakamakon da ya dace, wanda ya faɗo daga saman dutse sai ya kashe kansa to shi yana cikin wutar Jahannama zai dinga faɗowa a cikinta daga dutsen Jahannama zuwa kwarinta yana madawwami a cikinta, wanda ya kwankwɗi wata guba sai ya kashe kansa da ita to gubarsa tana hannunsa zai dinga kwankwaɗarta a cikin wutar Jahannama yana madawwami a cikinta har abada, wanda ya cakawa kansa wani karfe a cikinsa sai ya kashe kansa, to karfensa yana hannunsa zai dinga sukar kansa da shi a cikinsa a cikin wutar Jahannama yana madawwami a cikinta har abada.

Fa'idoji

  • Haramcin mutum ya kashe kansa, kuma cewa shi yana daga cikin manyan zunuban da yake cancantar azaba mai raɗaɗi da su.
  • Abinda ya ambata a cikin hadisin buga misali ne ga wasu daga cikin nau'ikan kashe rai, inba haka ba to ta kowace hanaya ya kashe rai za’a yi masa uƙuba da kwatankwacin abinda ya aikatawa kansa, haƙiƙa faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo a cikin Sahihul Bukhari cewa: «Wanda ya shaƙe kansa zai shaƙe shi a cikin wuta, wanda kuma ya soke kansa to zai sokeshi a cikin wuta».
  • Nawawi ya ce: Amma faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: (To shi yana cikin wutar Jahanama yana madawwami a cikinta har abada); sai aka ce: A cikinsa akwai maganganu, na farkonsu: Cewa shi abin ɗauka ne akan wanda ya aikata hakan yana mai halattawa tare da saninsa da haramcin to wannan kafiri ne, wannan kuma ita ce uƙubarsa. Na biyu: Cewa abin nufi da dawwama ita ce tsawon dadewa da kuma zaman da za'a tsawaita ba wai haƙiƙanin dawwamar ba, kamar yadda ake cewa: Allah Ya dawwamar da mulkin sarki. Na uku: Cewa wannan shi ne sakamakonsa, sai dai (Allah) tsarki ya tabbatar maSa ya daukaka ya yi baiwa sai Ya bada labarin cewa wanda ya mutu yana musulmi ba zai dawwama a cikin wuta ba.
  • Wannan yana daga babin tabbatar da jinsin uƙubobin lahira ga laifukan duniya, kuma ana fahimta daga gare shi cewa laifin mutum yana kan kansa kamar laifin waninsa ne akan waninsa a zunubi; domin cewa ransa ba mallakinsa bane kai tsaye, kai shi na Allah ne - Maɗaukakin sarki -, ba'a tasarrufi a cikinsa sai da abinda Ya yi masa izini a cikinsa.
Sharhi: العربية

حذر النبي صلى الله عليه وسلم من تعمَّد قتْل نفسه بالدنيا فإنه يعاقب يوم القيامة في نار جهنم بنفس الطريقة التي فعلها بنفسه في الدنيا جزاءً وفاقًا، فمن أسقط نفسه من فوق جبل فقتلها فهو في نار جهنم يسقط فيها من جبال جهنم إلى أوديتها خالدًا مخلدًا فيها أبدًا، ومن تجرع سمًّا فقتل نفسه به فسمه في يده يتجرعه في نار جهنم خالدًا مخلدًا فيها أبدًا، ومن ضرب نفسه بحديدة في بطنه فقتلها، فحديدته في يده يطعن بها في بطنه في نار جهنم خالدًا مخلدًا فيها أبدًا.

  • تحريم قتْل الإنسان نفسه، وأنه من كبائر الذنوب التي يستحق بها العذاب الأليم.
  • ما ذكره في الحديث هو ضربُ مثل لبعض أنواع إزهاق النفس، وإلا فبأي طريقة قتلت عوقب بمثل ما فعل بنفسه، وقد جاء في صحيح البخاري قوله صلى الله عليه وسلم: "الذي يخنق نفسه يخنقها في النار، والذي يطعنها يطعنها في النار".
  • قال النووي: وأما قوله صلى الله عليه وسلم: (فهو في نار جهنم خالدًا مخلدًا فيها أبدًا)؛ ‏‏فقيل: فيه أقوال، أحدها: أنه محمول على من فعل ذلك مستحلًّا مع علمه بالتحريم فهذا كافر، وهذه عقوبته، والثاني: أن المراد بالخلود طول المدة والإقامة المتطاولة لا حقيقة الدوام، كما يقال: خلد الله ملك السلطان، والثالث: أن هذا جزاؤه، ولكن تكرم سبحانه وتعالى فأخبر أنه لا يخلد في النار من مات مسلمًا.
  • هذا من باب مجانسة العقوبات الأخروية للجنايات الدنيوية، ويؤخذ منه أن جناية الإنسان على نفسه كجنايته على غيره في الإثم؛ لأن نفسه ليست ملكًا له مطلقًا، بل هي لله تعالى، فلا يتصرف فيها إلا بما أذن له فيه.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari