Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ أَبِي الدَّرْدَاءِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَلاَ أُخْبِرُكُمْ بِأَفْضَلَ مِنْ دَرَجَةِ الصِّيَامِ وَالصَّلاَةِ وَالصَّدَقَةِ؟» قَالُوا: بَلَى، قَالَ: «صَلاَحُ ذَاتِ البَيْنِ، فَإِنَّ فَسَادَ ذَاتِ البَيْنِ هِيَ الحَالِقَةُ».
Fassara
Daga Abu al-Darda'i - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Shin bana baku labarin abin da ya fi azimi da sallah da sadaka daraja ba?" Suka ce: Eh, ya ce: "Yin sulhu tsakanin waɗanda ke rigima, domin ɓacin tsakanin waɗanda ke rigima shine mai askewa".
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambayi sahabbansa: Shin bana baku labarin abin da ya fi ladan nafilar azimi da sallah da sadaka ba? Suka ce: Eh.. Ya ce: Yin sulhu tsakaknin masu rigima inda rigima take gadar da rabuwa da kuma kadaita da ƙiyayya da juyawa juna baya tsakanin mutane, domin abin da yake haifuwa akan ɓata waɗanda ke rigima na ƙiyayya wacce ita ce ɗabi'ar da sha'aninta shine ta halakar ta tunɓuke Addini da duniya kamar yadda aska take tunɓuke gashi.
Fa'idoji
- Shiryarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta hanyar tambayar sahabbai da kuma sasu shauƙin sanin amsa.
- Ɗaibi ya ce: Kwaɗaitarwa a kan sulhunta masu rigima da nisantar ɓata su; domin yin sulhu sababi ne na yin riƙo da igiyar Allah da kuma rashin rabuwa tsakanin musulmai, ɓacin masu rigima rabuwa ne a cikin Addini duk wanda ya yi sulhu ya kuma ɗauke ɓacinta zai samu daraja sama da abin da mai azimi mai tsayuwar dare mai shagalta da keɓantuwar kansa yake samu.
Sharhi: العربية
سأل النبي صلى الله عليه وسلم أصحابه: هل أخبركم بأفضل من أجر الإكثار من نافلة الصيام والصلاة والصدقة؟ قالوا: نعم. قال: الإصلاح بين المتخاصمين حيث تورث الخصومة الفرقة والوحشة والتباغض والتدابر بين الناس، فإنَّ ما يترتب على فساد ذات البين من البغضاء هي الخصلة التي من شأنها أن تهلك وتستأصل الدين والدنيا كما يستأصل الموسى الشعر.
- هدي النبي صلى الله عليه وسلم بسؤال الصحابة وتشويقهم لمعرفة الجواب.
- قال الطيبي: الحث والترغيب في إصلاح ذات البين واجتناب إفسادها؛ لأن الإصلاح سبب للاعتصام بحبل الله وعدم التفرق بين المسلمين، وفساد ذات البين ثلمة في الدين فمن تعاطى إصلاحها ورفع فسادها نال درجة فوق ما يناله الصائم القائم المشتغل بخاصة نفسه.