Hadisai

Shin kun san mai Ubangijinku Ya ce?" Suka ce: Allah da Manzonsane mafi sani, ya ce: "Mumini da kafiri sun wayi gari daga bayina

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ زَيْدِ بْنِ خَالِدٍ الجُهَنِيِّ رضي الله عنه أَنَّهُ قَالَ: صَلَّى لَنَا رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ صَلَاةَ الصُّبْحِ بِالْحُدَيْبِيَةِ عَلَى إِثْرِ سَمَاءٍ كَانَتْ مِنَ اللَّيْلَةِ، فَلَمَّا انْصَرَفَ أَقْبَلَ عَلَى النَّاسِ، فَقَالَ: «هَلْ تَدْرُونَ مَاذَا قَالَ رَبُّكُمْ؟» قَالُوا: اللهُ وَرَسُولُهُ أَعْلَمُ، قَالَ: «أَصْبَحَ مِنْ عِبَادِي مُؤْمِنٌ بِي وَكَافِرٌ، فَأَمَّا مَنْ قَالَ: مُطِرْنَا بِفَضْلِ اللهِ وَرَحْمَتِهِ، فَذَلِكَ مُؤْمِنٌ بِي وَكَافِرٌ بِالْكَوْكَبِ، وَأَمَّا مَنْ قَالَ: بِنَوْءِ كَذَا وَكَذَا، فَذَلِكَ كَافِرٌ بِي وَمُؤْمِنٌ بِالْكَوْكَبِ».

Fassara

Daga Zaidu Dan Khalid AlJuhani - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mana sallar Asuba a Hudaibiyya a bayan (ruwan daya sauka) a wannan daren da ya wuce, lokacin da ya sallame sai ya juya ya fuskanto mutane, ya ce: "Shin kun san mai Ubangijinku Ya ce?" Suka ce: Allah da Manzonsane mafi sani, ya ce: "Mumini da kafiri sun wayi gari daga bayina" Amma wanda ya ce: An yi mana ruwa da falalar Ubangiji da rahamarSa, to wannan ya yi imani da Ni, kuma ya kafircewa taurari. Amma wanda ya ce: Da tauraro kaza da kaza, to wannan ya kafirce mi Ni kuma ya yi imani da taurari".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi sallar Asuba a Hudaibiyya - ita wata alkaryace kusa da Makka bayan wani ruwa da ya sauka a wannan daren, Lokacin da ya yi sallama ya idar da sallarasa sai ya fuskanto mutane da fuskarsa, sai ya tambayesu: Shin kun san me Ubangijinku - Mai girma da daukaka - Ya ce ? Sai suka amsa masa: Allah da ManzonSane mafi sani. Sai ya ce: Lallai Allah - Madaukakin sarki - Ya bayyana cewa mutane a lokacin saukar ruwa sun kasu gida biyu: Bangare daya sun yi imani da Allah - Madaukakin sarki -, daya bangaren kuma suka kafircewa Allah - Madaukakin sarki -; Amma wanda ya ce: An yi mana ruwa da falalar Allah da rahamarSa, ya danganta saukar ruwa ga Allah - Madaukakin sarki -; to wannan ya yi imani da Allah Mahalicci Mai jujjuya al'amura a cikin halittarsa , kuma ya kafircewa taurari. To amma wanda ya ce: An yi mana ruwa da tauraro iri kaza da kaza; to wannan ya kafircewa Allah kuma ya yi imani da taurari, shi karamin kafarcine ta inda ya danganta saukar ruwa ga taurari; kuma Allah bai sanya shi wani sababi na shari'a ba ko na kaddara, Amma wanda ya danganta saukar ruwa da waninsa daga fararrun abubuwa na kasa ga motsin taurari a bullowarsu da faduwarsu yana mai kudire cewa su ne masu aikin na hakika to shi kafirine kafirci babba.

Fa'idoji

  • Anso fadin: An yi mana ruwa da falalar Allah da rahamarSa bayan saukar ruwa.
  • Wanda ya danganta ni'imar saukar ruwa da wasunsu ga taurari a halitta da samarwa to shi kafirine kafirci babba, idan ya danganta shi akan cewa shi wani sababi ne to shi kafirine kafirci karami domin cewa shi ba sababi ne na shari'a ko na gani ba.
  • Lallai ni'ima tana kasancewa sababi na kafirci idan an butulce, kuma tana zama sababi na imani idan an gode.
  • Hani akan fadin: "An yi mana ruwa da tauraro kaza da kaza", koda an nufi lokaci; dan toshe kafar shirka.
  • Wajabcin damfarar zuciya ga Allah - Madaukakin sarki - a jawo ni'imomi da tunkude bala’o’i.
Sharhi: العربية

صلى النبي صلى الله عليه وسلم صلاة الصبح بالحديبية -وهي قرية قريبة من مكةـ بعد مطر نزل في تلك الليلة، فلما سلم وانتهى من صلاته أقبل على الناس بوجهه، فسألهم: هل تدرون ماذا قال ربكم عز وجل؟ فأجابوه: الله ورسوله أعلم، فقال: إن الله تعالى بَيًّن أن الناس ينقسمون عند نزول المطر إلى قسمين: قسم مؤمن بالله تعالى، وقسم كافر بالله تعالى؛ فأما من قال: مطرنا بفضل الله ورحمته، ونَسَب إنزال المطر إلى الله تعالى؛ فذلك مؤمن بالله الخالق المتصرف في الكون، وكافر بالكوكب. وأما من قال: مطرنا بنجم كذا وكذا؛ فذلك كافر بالله، مؤمن بالكوكب، وهو كفر أصغر حيث نسب إنزال المطر إلى الكوكب؛ والله لم يجعله سببًا شرعيًا ولا قدريًّا، وأما من نسب نزول المطر وغيره من الحوادث الأرضية إلى تحرُّكات الكواكب في طلوعها وسقوطها معتقدًا أنها الفاعل الحقيقي، فهو كافر كفرًا أكبر.

  • استحباب القول بعد نزول المطر: مُطرنا بفضل الله ورحمته.
  • من نسب نعمة إنزال المطر وغيرها إلى الكوكب خَلْقًا وإيجادًا فهو كافرٌ كفرًا أكبر، وإن نسبه على أنه سببٌ فهو كافرٌ كفرًا أصغر لأنه ليس بسبب شرعي ولا حسي.
  • أن النعمة تكون سببًا للكفر إذا كُفِرت، وتكون سببًا للإيمان إذا شُكرت.
  • النهي عن قول: "مطرنا بنوء كذا"، ولو قُصِد بها الوقت؛ سدًّا لذريعة الشرك.
  • وجوب تعلُّق القلب بالله تعالى في جَلْب النعم ودفع النقم.
  • هذا الحديث مما يرويه النبي صلى الله عليه وسلم عن ربه، ويسمى بالحديث القدسي أو الإلهي، وهو الذي لفظه ومعناه من الله، غير أنه ليست فيه خصائص القرآن التي امتاز بها عما سواه ، من التعبد بتلاوته والطهارة له والتحدي والإعجاز وغير ذلك.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari