Hadisai

Babu wani musulmin da wata musiba zata same shi, sai ya faɗi abinda Allah Ya umarce shi: {Lallai mu daga Allah muke kuma lallai cewa mu zuwa ga Allah zamu koma} [al-Baƙara: 156], ya Allah Ka bani lada a cikin wannan musibar tawa kuma Ka musanya mini da mafi alheri da ita, sai Allah Ya musanya masa da mafi alheri daga ita

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أُمِّ سَلَمَةَ أُمِّ المؤْمنينَ رَضيَ اللهُ عنها أَنَّهَا قَالَتْ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم يَقُولُ: «مَا مِنْ مُسْلِمٍ تُصِيبُهُ مُصِيبَةٌ فَيَقُولُ مَا أَمَرَهُ اللهُ: {إِنَّا لِلهِ وَإِنَّا إِلَيْهِ رَاجِعُونَ} [البقرة: 156]، اللَّهُمَّ أْجُرْنِي فِي مُصِيبَتِي، وَأَخْلِفْ لِي خَيْرًا مِنْهَا، إِلَّا أَخْلَفَ اللهُ لَهُ خَيْرًا مِنْهَا»، قَالَتْ: فَلَمَّا مَاتَ أَبُو سَلَمَةَ قُلْتُ: أَيُّ الْمُسْلِمِينَ خَيْرٌ مِنْ أَبِي سَلَمَةَ؟ أَوَّلُ بَيْتٍ هَاجَرَ إِلَى رَسُولِ اللهِ صلى الله عليه وسلم، ثُمَّ إِنِّي قُلْتُهَا، فَأَخْلَفَ اللهُ لِي رَسُولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم.

Fassara

Daga Ummu Salamah Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Babu wani musulmin da wata musiba zata same shi, sai ya faɗi abinda Allah Ya umarce shi: {Lallai mu daga Allah muke kuma lallai cewa mu zuwa ga Allah zamu koma} [al-Baƙara: 156], ya Allah Ka bani lada a cikin wannan musibar tawa kuma Ka musanya mini da mafi alheri da ita, sai Allah Ya musanya masa da mafi alheri daga ita", ta ce: Lokacin da Abu Salama ya rasu na ce: Waye a cikin musulmai ya fi Abu Salama alheri? farkon gidan da ya yi hijra zuwa ga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sannan sai na faɗeta (addu'ar), sai Allah Ya maye mini gurbinsa da manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

Sharhi

Uwar muminai Ummu Salama - Allah Ya yarda da ita - ta ambaci cewa ita ta ji manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa wata rana: Babu wani musulmin da wata musiba zata same shi sai ya faɗi abinda Allah Ya so gare shi: {Lallai mu daga Allah muke kuma lallai mu zuwa ga Allah zamu koma} [al-Baƙara: 156], (Ya Allah Ka bani lada) Ka bani ladan haƙurina (a cikin wannan musiba), ka canja mini (Ka maye mini gurbi) daga ita (da mafi alheri daga gareta); sai Allah Ya canja masa mafi alheri daga gareta. Ta ce : Lokacin da Abu Salama ya yasu na ce: Waye cikin musulmai ya fi Abu Salama alheri?! farkon gidan da ya yi hijira zuwa ga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sannan Allah Ya taimake ni sai na faɗeta, sai Allah Ya maye mini gurbin Abu Salama da manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbta agare shi -.

Fa'idoji

  • Umarni da haƙuri a lokacin musibu da kuma rashin kururuwa.
  • Fuskantar da addu'a zuwa ga Allah a cikin musibu da suke sauka; domin canji yana gare shi (shi Allah).
  • Larurar mumini ya yi ruko da umarnin annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - koda hikima bata bayyana daga umarninsa ba.
  • Alheri dukkansa yana cikin ruko da umarnin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Sharhi: العربية

ذكرت أم المؤمنين أم سلمة رضي الله عنها أنها سمعت النبي صلى الله عليه وسلم يقول ذات مرة: ما من مسلم تصيبه مصيبة فيقول ما استحبّه الله له: {إِنَّا لِلهِ وَإِنَّا إِلَيْهِ رَاجِعُونَ} [البقرة: 156]، (اللهم أجرني) وأعطني أجر صبري (في مصيبتي)، وعوضني (وأخلف لي) عنها (خيرًا منها)؛ إلا عوّضه الله خيرًا منها. قالت: فلما مات أبو سلمة قلت: من من المسلمين خيرٌ من أبي سلمة؟! أول بيت هاجر إلى رسول الله صلى الله عليه وسلم، ثم إني أعانني الله فقلتها، فأخلف الله لي رسولَ الله صلى الله عليه وسلم خير من أبي سلمة.

  • الأمر بالصبر عند المصائب وعدم الجَزَع.
  • التوجّه بالدعاء إلى الله في المُلِمّات؛ لأن عنده العوض.
  • ضرورة امتثال المؤمن لأمر النبي صلى الله عليه وسلم وإن لم تظهر له الحكمة من أمره.
  • الخير كله في امتثال المؤمن لأمر النبي صلى الله عليه وسلم.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari