Hadisai

Iyalan (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba su taɓa cin abinci sau biyu a rana ɗaya ba sai ɗayansu ya zama dabino ne

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤْمِنينَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا قَالَتْ: مَا أَكَلَ آلُ مُحَمَّدٍ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَكْلَتَيْنِ فِي يَوْمٍ إِلَّا إِحْدَاهُمَا تَمْرٌ.

Fassara

Daga Nana A'isha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Iyalan (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba su taɓa cin abinci sau biyu a rana ɗaya ba sai ɗayansu ya zama dabino ne.

Sharhi

Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - tana bada labarin cewa iyalan gidan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - basu taɓa cin abinci sau biyu ba a rana ɗaya sai ɗayan ya zama dabino ne.

Fa'idoji

  • Tawali'un Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da iyalan gidansa, sauda yawa a rana ɗaya ma basu samun wani abin da zasu ci sai abinci ɗaya.
  • Dabino ya kasance shine mafi sauƙi a wurinsu akan waninsa.
  • Falalar gudun duniya da wadatuwa da kaɗan a rayuwa, kuma kasancewarsa yana daga ɗabi'un Annabawa, da kuma tarihin shugaban Manzanni.
  • Cin abinci sau biyu a rana ɗaya yana daga cikin al'amuran da aka halatta, kuma hakan yana daga cikin sanannun al'adun larabawa, domin sun kasance a rana ɗaya suna ci ne sau biyu, abincin rana da abincin dare.
Sharhi: العربية

تُخبر أم المؤمنين عائشة رضي الله عنها أن أهل بيت النبي صلى الله عليه وسلم لم يأكلوا وجبتين في يوم واحد إلا كانت إحدى الوجبتين هي التمر.

  • تواضع النبي صلى الله عليه وسلم وأهل بيته، فربما لم يجدوا في اليوم إلا أكلة واحدة.
  • التمر كان أيسر عندهم من غيره.
  • فضيلة الزهد والاكتفاء بالقليل من العيش، وكونه من أخلاق النبيين، وسيرة سيد المرسلين.
  • تناول الطعام مرتين في اليوم الواحد من الأمور المباحة الجائزة، وهو من عادات العرب المعروفة، كانوا يأكلون في اليوم أكلتين، أكلة الغداء، وأكلة العشاء.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari