Hadisai

Lokacin rasuwar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai bar dirhami ko dinari ko bawa ko baiwa ko wani abu ba sai farar alfadararsa da makaminsa, da wani filin da ya maida shi sadaka

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ عَمْرِو بْنِ الحَارِثِ خَتَنِ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَخِي أُمِّ المؤمِنين جُوَيْرِيَةَ بِنْتِ الحَارِثِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُم، قَالَ: مَا تَرَكَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عِنْدَ مَوْتِهِ دِرْهَمًا وَلاَ دِينَارًا وَلاَ عَبْدًا وَلاَ أَمَةً وَلاَ شَيْئًا، إِلَّا بَغْلَتَهُ البَيْضَاءَ، وَسِلاَحَهُ، وَأَرْضًا جَعَلَهَا صَدَقَةً.

Fassara

Daga Amr Ibul Haris ɗan uwan mai dakin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ɗan uwar ummul muminina Juwairiyya Bintul Haris - Allah Ya yarda da su -, ya ce: Lokacin rasuwar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai bar dirhami ko dinari ko bawa ko baiwa ko wani abu ba sai farar alfadararsa da makaminsa, da wani filin da ya maida shi sadaka.

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya rasu bai bar dirhamin na azirfaba ko zinari ba, ko bawan da ya mallaka ko baiwar da ya mallaka ko raƙumi ko wani abu na dukiyaba, sai kawai farar alfadararsa wacce yake hawanta, da wani filin da ya bar shi waƙafi a lokacin da yake da lafiya saboda matafiya.

Fa'idoji

  • Annabawa ba'a gadarsu.
  • Bayanin abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bari bayan mutuwarsa.
  • (Annabi) tsira da amincin su tabbata agare shi ya rasu amma bai bar wani abin da yake da kima ba, saboda kyautarsa da kuma ciyarwarsa da kuma kyautatawarsa.
  • Karmani ya ce: Wakilin suna a cikin faɗinsa (kuma ya sanyata) mai komawa ne ga duka ukun wato alfadarar da makami da fili bawai zuwa filin kawai ba.
  • Al-Khitn: Ɗan'uwar mata, al-Ukhtani kuma ta ɓangaren mace.
Sharhi: العربية

توفي النبي صلى الله عليه وسلم ولم يترك لا درهم فضة ولا دينار ذهب، ولا عبدًا مملوكًا ولا أمة مملوكة، ولا شاة ولا بعيرًا ولا شيئًا من المال، إلا بغلته البيضاء التي كان يركبها، وسلاحه الذي كان يحمله، وأرضًا أَوْقَفها في صحته لابن السبيل.

  • الأنبياء لا يورثون.
  • بيان ما ترك النبي صلى الله عليه وسلم بعد موته.
  • تُوفي عليه الصلاة والسلام وما ترك شيئًا له أهمية، من جوده وإنفاقه وإحسانه.
  • قال الكرماني: الضمير في قوله (وجعلها) راجع إلى الثلاث أي البغلة والسلاح والأرض لا إلى الأرض فقط.
  • الختن: أخو الزوجة، والأختان من قبل المرأة.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari