Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عن ابْنِ عُمَرَ رَضيَ اللهُ عنهُما قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَيُّمَا امْرِئٍ قَالَ لِأَخِيهِ: يَا كَافِرُ، فَقَدْ بَاءَ بِهَا أَحَدُهُمَا، إِنْ كَانَ كَمَا قَالَ، وَإِلَّا رَجَعَتْ عَلَيْهِ».
Fassara
Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Duk mutumin da ya cewa ɗan'uwansa: Ya kai kafiri, to haƙiƙa ɗayansu ya dawo da ita (ya lazimceta), idan ya zama kamar yadda ya ce ne, inba haka bafa to zata dawo kansa".
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargaɗar da musulmi ya ce wa ɗan'uwansa musulmi: Ya kai kafiri, to haƙiƙa ɗayansu ya cancanci kalmar kafircin, idan ya kasance kamar yadda ya faɗa ne, inba haka ba kafirtawar da ya yi wa ɗan'uwansa za ta dawowa wanda ya fada.
Fa'idoji
- Tsawatarwa musulmi akan ya faɗawa ɗan'uwansa musulmi abinda babu a cikinsa na siffofin fasiƙanci da kuma kafirci.
- Gargaɗarwa daga wannan mummunar maganar, kuma cewa mai ita yana kan haɗari mai girma idan ya faɗeta ga ɗan'uwansa, to yana kamata kiyaye harshe kuma kada ya yi magana sai da tunani.
Sharhi: العربية
حذَّر النبيُّ صلى الله عليه وسلم من أن يقول المسلم لأخيه المسلم: يا كافر، فقد استحق بكلمة الكفر أحدهما، إن كان كما قال، وإلا رجع على القائل تكفيره لأخيه.
- زجر المسلم عن أن يقول لأخيه المسلم ما ليس فيه من صفات الفسوق والكفر.
- التحذير من هذا الكلام السيئ، وأن صاحبه على خطر عظيم إذا قاله لأخيه، فينبغي حفظ اللسان وأن لا يتكلم إلا عن بصيرة.