Hadisai

(Mutum) bakwai Allah - Maɗaukakin sarki - Zai inuwantar da su a cikin inuwarSa ranar da babu wata inuwa sai inuwarSa

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «سَبْعَةٌ يُظِلُّهُمُ اللَّهُ تَعَالَى فِي ظِلِّهِ يَوْمَ لاَ ظِلَّ إِلَّا ظِلُّهُ: إِمَامٌ عَدْلٌ، وَشَابٌّ نَشَأَ فِي عِبَادَةِ اللَّهِ، وَرَجُلٌ قَلْبُهُ مُعَلَّقٌ فِي المَسَاجِدِ، وَرَجُلاَنِ تَحَابَّا فِي اللَّهِ، اجْتَمَعَا عَلَيْهِ وَتَفَرَّقَا عَلَيْهِ، وَرَجُلٌ دَعَتْهُ امْرَأَةٌ ذَاتُ مَنْصِبٍ وَجَمَالٍ فَقَالَ: إِنِّي أَخَافُ اللَّهَ، وَرَجُلٌ تَصَدَّقَ بِصَدَقَةٍ فَأَخْفَاهَا حَتَّى لاَ تَعْلَمَ شِمَالُهُ مَا تُنْفِقُ يَمِينُهُ، وَرَجُلٌ ذَكَرَ اللَّهَ خَالِيًا، فَفَاضَتْ عَيْنَاهُ».

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «(Mutum) bakwai Allah - Maɗaukakin sarki - Zai inuwantar da su a cikin inuwarSa ranar da babu wata inuwa sai inuwarSa: Shugaba adali, da saurayin da ya taso a cikin bautar Allah, da mutumin da zuciyarsa ta rataya da masallatai, da mutum biyu da suka so juna saboda Allah, sun haɗu saboda Shi kuma suka rabu saboda Shi, da mutumin da mace mai matsayi da kyau ta neme shi sai ya ce: Lallai ni ina jin tsoron Allah, da mutumin da ya yi sadaka sai ya ɓoyeta har (hannunsa) na hagu bai san abinda (hannunsa) na dama ya ciyar ba, da mutumin da ya ambaci Allah shi kaɗai sai idanuwansa suka zubar da hawaye».

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa nau'i bakwai na muminai bushara cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Zai inuwantar da su a inuwar al-ArshinSa a ranar da babu wata inuwa sai inuwarSa: Na farko: Shugaba adali a kansa ba fasiƙi ba, kuma mai adalci tsakanin talakawansa ba azzalimi ba; shi ne babban shugaba, dukkan wanda ya jiɓinci wani abu na al'amuran musulmai sai ya yi adalci a cikinsa zai risku da hakan. Na biyu: Saurayin da ya taso a cikin bautar Allah, kuma ya ƙarar da samartakarsa da nishaɗinsa, har ya mutu akan hakan. Na uku; Mutumin da zuciyarsa ta rataya da masallaci idan ya fita daga cikinsa har sai ya dawo zuwa gare shi, saboda tsananin soyayyarsa gare shi da kuma lazimtar masallacin da ci gaba da kasancewa a cikinsa da zuciya, koda wani abu mai bijirowa ya bijirowa jiki (kamar rashin lafiya) kuma ya zama a wajen masallacin. Na huɗu; Mutum biyu kowane ɗaya daga cikinsu ya so ɗayan saboda Allah a haƙiƙa, kuma suka dawwama akan soyayyar Addini wani abu mai bijirowa na duniya bai rabasu ba daidai ne sun haɗu a haƙiƙa ko a'a har mutuwa ta rabasu. Na biyar: Da mutumin da mace ta neme shi akan kanta dan aikata alfasha, kuma mai asali ce da ɗaukaka da matsayi da alfarma da dukiya da kyau, sai ya ƙi kuma ya ce: Ni ina jin tsoron Allah. Na shida: Mutumin da ya yi sadaka kaɗan ce ko mai yawa bai yi riya a cikinta ba kai ya ɓoyeta har hagunsa bata sanin abinda damansa take ciyarwa. Na bakwai: Mutumin da ya ambaci Allah da zuciyarsa daga tinani ne, ko da harshensa na zikiri, a keɓance daga mutane sai hawaye suka kwaranyo daga idanuwansa dan jin tsoron Allah da kuma girmama Shi - Maɗaukakin sarki -.

Fa'idoji

  • Falalar nau'i bakwan da aka mabata da kwaɗaitarwa akan koyi da su.
  • Ibnu Hajar ya ce a cikin faɗinsa: "A cikin inuwarSa": An ce abinda ake nufi: Inuwar Al’arshinsa, Hadisin Salman yana nuni a kansa daga (riwayar) Sa'id ɗan Mansur da Isnadi kykkyawa: "Mutum bakwai Allah Zai inuwantar da su a cikin inuwar al-ArshinSa".
  • Ibnu Hajar ya ce: Mafi kyan abinda aka fassara mai adalci da shi cewa shi ne wanda yake bin umarnin Allah ta hanyar ajiye kowane abu a bigiransa ba tare da wuce gona da iri ko sakaci ba, kuma ya gabatar da shi a ambato dan gamewar amfanin da shi.
  • Falalar jiran sallah bayan sallah.
  • Nawawi ya ce: A cikinsa akwai kwaɗaitarwa akan soyayya saboda Allah da bayanin girman falalarta.
  • An keɓanci matsayi da kyau dan tsananin kwaɗayin mutane a cikinsu da kuma kwaɗayinsu a kansu, da wahalar samunsu.
  • Abinda ya fi a sadaka shi ne ɓoyewa da nisanta daga riya, duk da an halatta bayyanar da sadaka da zakka idan sun kuɓuta daga riya kuma aka nufi kwaɗaitar da wani akan ciyarwa kuma dan waninsa ya yi koyi da shi, da kuma bayyanar da alamomin Musulunci.
  • Kaɗai waɗannan mutum bakwan sun samu wannan ni'imar ce saboda ikhlasi ga Allah - Maɗaukakin sarki - da kuma saɓawa son rai.
  • Faɗinsa: "Mutum bakwai Allah Zai inuwantar da su": Taƙaitawarsu da wannan adadin ba abin nufi bane, kai wasun waɗannan nau'ikan sun zo a cikin hadisin daga waɗanda Allah Zai inuwantar da su a inuwar Al’ArshinSa.
  • Ibnu Hajar ya ce: Ambatan maza a cikin hadisin ba shi da wani abin fahimtar cewa su ake nufi kawai; kai mata ma suna tarayya tare da mazan a cikin ayyuka a abinda aka ambata, sai dai idan ana nufin shugaba adali wato babban shugabanci, inba haka ba to mace zata iya shiga tunda itama tana da iyalai kuma ta yi adalci a cikinsu, kuma ɗabi'ar lazimtar masallaci ta fitar da mace; domin cewa sallar mace a cikin gidanta ya fi ta yi a masallaci, abinda ke koma bayan hakan to tarayya da su ta tabbata, har namijin da mace ta neme shi shima ana suranta samun hakan a macen da sarki kyakkyawa ya nemeta a misali sai taƙi dan jin tsoron Allah - Madaukakin sarki - tare da cewa tana bukatar hakan.
Sharhi: العربية

بشّر النبي صلى الله عليه وسلم سبعة أصناف من المؤمنين يظلهم الله تعالى في ظل عرشه يوم لا ظل إلا ظله: الأول: إمام عدل في نفسه غير فاسق، عادل بين رعيته غير ظالم؛ وهو صاحب الولاية العظمى، ويلتحق به كل من ولي شيئًا من أمور المسلمين فعدل فيه. الثاني: شاب نشأ في عبادة الله، وأفنى شبابه ونشاطه، حتى توفي على ذلك. الثالث: رجل قلبه معلق بالمسجد، إذا خرج منه حتى يعود إليه لشدة حبه وكثرة ملازمة المسجد واستمرار الكون فيه بالقلب وإن عرض للجسد عارض وكان خارج المسجد. الرابع: رجلان أحب كلٌّ منهما الآخر في الله حقيقة، وداما على المحبة الدينية ولم يقطعاها بعارض دنيوي سواء اجتمعا حقيقة أم لا حتى فرق بينهما الموت. الخامس: ورجل طلبته امرأة إلى نفسها لفعل الفاحشة، وهي ذات أصل وشرف وحسب وجاه ومال وجمال، فأبى وقال لها: إني أخاف الله. السادس: رجل قد تصدق بصدقة قليلة أو كثيرة ولم يراءِ فيها بل أخفاها حتى لا تعلم شماله ما تنفقه يمينه. السابع: رجل ذكر الله بقلبه من التذكر، أو بلسانه من الذكر، في خلاء عن الناس ففاضت الدموع من عينيه خشية وتعظيمًا لله تعالى.

  • فضل الأصناف السبعة المذكورة والحث على الاقتداء بها.
  • قال ابن حجر في قوله "في ظله": قيل المراد: ظل عرشه، ويدل عليه حديث سلمان عند سعيد بن منصور بإسناد حسن "سبعة يظلهم الله في ظل عرشه".
  • قال ابن حجر: وأحسن ما فسر به العادل أنه الذي يتبع أمر الله بوضع كل شيء في موضعه من غير إفراط ولا تفريط، وقدّمه في الذكر لعموم النفع به.
  • فضل انتظار الصلاة بعد الصلاة.
  • قال النووي: فيه الحث على التحابّ بالله وبيان عظيم فضله.
  • خُصَّ المنصب والجمال لشدة رغبة الناس فيهما وحرصهم عليهما، وصعوبة حصولهما.
  • الأفضل في الصدقة الإسرار والأبعد من الرياء، وإن كان يشرع الجهر بالصدقة والزكاة إن سلمت عن الرياء وقصد بها حث الغير على الإنفاق وليقتدي به غيره، ولإظهار شعائر الإسلام.
  • إنما نال هؤلاء السبعة ذلك النعيم بالإخلاص لله تعالى ومخالفة الهوى.
  • قوله: "سبعة يظلهم الله": حصْرهم بهذا العدد ليس مرادًا، بل ورد غير الأصناف الواردة في الحديث ممن يظلهم الله بظل عرشه.
  • قال ابن حجر: ذكر الرجال في هذا الحديث لا مفهوم له؛ بل يشترك النساء معهم أي مع الرجال في الأعمال فيما ذكر، إلا إن كان المراد بالإمام العادل الإمامة العظمى، وإلا فيمكن دخول المرأة حيث تكون ذات عيال فتعدل فيهم، وتخرج خصلة ملازمة المسجد؛ لأن صلاة المرأة في بيتها أفضل من المسجد، وما عدا ذلك فالمشاركة حاصلة لهن، حتى الرجل الذي دعته المرأة فإنه يتصور في امرأة دعاها ملك جميل مثلًا فامتنعت خوفًا من الله تعالى مع حاجتها.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari