Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَدْخُلُ الْخَلَاءَ، فَأَحْمِلُ أَنَا وَغُلَامٌ نَحْوِي إِدَاوَةً مِنْ مَاءٍ وَعَنَزَةً فَيَسْتَنْجِي بِالْمَاءِ.
Fassara
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana shiga bayan gida, sai ni da wani yaro sa'ana mu ɗaukar masa salka ta ruwa da kuma sanda sai ya yi tsarki da ruwa.
Sharhi
Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa shi ya kasance da wani mai yin hidima sa'ansa a shekaru suna bin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - idan ya fita dan biyan buƙatarsa, suna ɗaukar masa sanda mai kai irin kan goron mashi dan ya sanyata kariya da zai rataya wani abu a kanta yana mai suturtawa ko kuma sutura ga sallarsa, kuma suna ɗaukar masa ƙaramar ƙwarya na fata wacce take a cike da ruwa, idan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gama biyan buƙatarsa sai ɗaya daga cikinsu ya ba shi ƙwaryar, sai ya yi tsarki da ruwa.
Fa'idoji
- Musulmi ya yi tanadin ruwan tsarki a lokacin biyan buƙata; dan kada ya buƙatar da shi zuwa tashi sai ya ɓata jikinsa.
- Kiyaye al'aura a lokacin biyan buƙata dan kada wani ya ganta; domin kallon al'aura haramun ne, ya kasance yana kafa sanda a ƙasa kuma yana shinfiɗa tufa mai suturtawa a kanta.
- Koyar da yara ladubban Musulunci da kuma tarbiyantar da su akanta; dan su gaje su (su saba da su).
Sharhi: العربية
يخبر أنس بن مالك رضي الله عنه أنه كان هو وخادم مقارب لسِنِّهِ يَتْبعان النبي صلى الله عليه وسلم إذا خرج لقضاء حاجته، يحملان معهما عصًا لها سنان مثل سنان الرمح ليجعلها سترة يعلق عليها شيء ساتر أو سترة لصلاته، ويحملان معهما أيضًا إناء صغير من جلد مملوءًا بالماء، فإذا فرغ النبي صلى الله عليه وسلم من قضاء حاجته ناوله أحدهما الإناء، فيستنجي بالماء.
- استعداد المسلم بطَهوره عند قضاء الحاجة؛ لئلا يُحْوِجَه إلى القيام فيتلوّث.
- حفظ العورة عند قضاء الحاجة عن أن ينظر إليها أحد؛ لأن النظر إلى العورة محرم، فكان يركز العصا في الأرض وينصب عليها الثوب الساتر.
- تعليم الأبناء الآداب الإسلامية وتربيتهم عليها؛ ليتوارثوها.
Maudu'ai
- FIƘHU DA USULU
- FALALOLI DA LADUBBA
- SIRA DA TARIHI
- FIƘHU NA IBADA
- TSARKI
- FALALOLI
- FALALOLIN SAHABBAI ALLAH YA YARDA DA SU
- SIRAR ANNABI
- MASU YI MASA HIDIMA TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARESHI
- ƊABI'U IRIN NA (ANNABI) MUHAMMAD
- GUSAR DA NAJASA
- LADUBBAN BIYAN BUƘATA
- TSARIN ANNABI
- TSARINSA TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARESHI A YIN TSARKI